Online counter

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihaR

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihaR

LABARAI DAGA 24BLOG
Zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata bai inganta ba a yayin da hukumar zabe ta kasa watau INEC tayi watsi da shi sakamakon dambarwar da ta auku yayin gudanar sa kama daga tashin-tashina ta 'yan baranda da kuma kwacen akwatin zabe.
Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun

Ganduje da Badaru sun ziyarci jihar Osun kan sakamakon Zaben Gwamnan jihar Osun

A yayin da ake ci gaba da zaman kirdadon sakamakon zaben gwamnan jihar da yau hukumar zabe ta sake gudanarwa, akwai wasu jiga-jigan kasar nan da suka kwashi kafafunsu har zuwa jihar domin kashe kwarkwatar idanunsu da hausawa kan ce gani ya kori ji da zasu kasance ganau ba jiyau ba.
Ire-iren wannan jiga-jigai da suka yi tattaki har zuwa jihar ta Osun sun hadar da; gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, Ministan watsa labarai da al'adu; Lai Muhammad, zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da sauransu.
Gwamnan jihar ta Osun, Rauf Aregbesola tare da Mataimakin sa, Sanata Iyiola Omisore, sun karrama wannan manyan baki yayin da suke zaman kirdadon sakamakon zaben a fadar gwamnatin su dake babban birnin jihar na Osogbo.
akwai kyakkyawan zato dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Gboyega Oyetola, shi zai lashe wannan zabe da yake kan gaba wajen samun nasara yayin da hukumar INEC ke ci gaba da kidayar kuri'u da bayyana sakamakon ta dalla dalla

Post a comment

0 Comments