Online counter

Fitar da dan takara: Sakamakon zaben Buhari daga jihohi 5

Fitar da dan takara: Sakamakon zaben Buhari daga jihohi 5

A jiya ne jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da zaben tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2019.
Kamar yadda jam’iyya ta bayyana a baya, ta gudanar da zaben shugaban Buhari kai tsaye, ma’ana kato bayan kato.
Duk da kasancewarsa dan takarar daya tilo daya sayi fam din takarar shugaban kasa a APC, jam’iyyar ta ce sai ta gudanar da zabukan tabbatar da shi a fadin jihohin kasar nan domin yin biyayya ga siyasa da kuma nunawa duniya farin jinin da shugaban keda shi har yanzu a tsakanin mambobin jam’iyyar APC.
1. Kano
Da yake sanar da sakamakon zaben jiya a Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar shugaba Buhari ya sanu adadin kuri’u 2,931,235 daga ‘yan jam’iyyar APC dake fadin kananan hukumomi 44 a jihar Kano.

2. Imo
A jihar Imo, jami’in kula da zaben Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa a APC, Cif Charles Amadi ya sanar da cewar shugaba Buhari ya samu kuri’u 697,532 daga cikin adadin ‘yan jam’iyyar 944,843 dake da cikin rijistar mambobin APC a Imo.
3. Zamfara
Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara yasanar da cewar shugaba Buhari ya samu kuri’u 247,847 daga cikin mambobin APC 251,600 da aka tantance domin yin zaben. Adadin kuri’un ya nuna cewar Buhari ya samu kaso 98% na kuri’un mambobin jam’iyyar APC a jihar Zamfara.
4. Bauchi
Shugaba Buhari ya samu kuri’u 700,086 daga cikin mambobin APC 800,085 da aka tantance domin yin zaben na jiya.
Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ne ya sanar da sakamakon zaben a yau, Asabar, da misalign karfe 2:00 na safe (daren Asabar).
5. Katsina
An tantance mambobin jam’iyyar APC 926,285 domin kada kuri’a a zaben tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa a APC. Buhari ya samu kuri’u 802,819, kamar yadda gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar.

Post a comment

0 Comments