Online counter

EFCC ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan PDP

EFCC ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan PDP
-labarai daga 24blog
A yau, Talata, ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kammala gabatar da hujjojin cin hanci a kan tsohon gwamnan jihar Oyo, Rasheed Ladoja, a gaban kotun tarayya dake Legas.
Ana tuhumar tsohon gwamna Ladoja da kwamishinansa na kudi, Waheed Akanbi, da badakalar kudi da yawansu ya kai biliyan N4.7bn daga asusun jihar Oyo.
A yayin da kotun ta zauna a yau, Talata, lauyoyin dake kare wadanda aka tuhuma sun sanar da kotu cewar wadanda suke karewar basu da laifi.
An fara gurfanar da Ladoja da Akanbi a gaban kotun mai shari'a, Mohammed Idris, a ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 2016.
Sai dai dukkan su sun musanta zargin tuhumar da ake masu.
Mai shari'a Idris ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin bayyana matsayin kotu a kan hujjojin da kowanne yanki ya gabatar.
KARANTA WANNAN;AMBALIYAR RUWA TAYI SANADIYAR MUTUWAR MUTANE DA YAWA A KANO
A wani labarin 24blog.com.ng, kun ji cewar gwamnan jihar Zamfar, Abdulaziz Yari, ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Sanata da zai wakilicin yammacin Zamfara a majalisar dattijai.
Sai dai a yayin da wasu ke ganin gwamna Yari zai fafata neman kujerar ne da tsohon maigidansa, Sanata Abdullahi Sani Yarima, sai ga shi jaridar Tribune ta rawaito cewar Yariman ya janyewa gwamna Yari takarar kujerar sanatan yankin da suka fito, yammacin jihar Zamfara.

Post a comment

0 Comments