LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 202,599 a zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da ya gudana a gundumomi 287 da ke cikin kananan hukumomi 27 na jihar Jigawa.
Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawam wanda shi ne jami'in tattara sakamako da sanar da shi na zaben, ya bayyana hakan a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Juma'a 28 ga watan satumba a garin Dutse.
Badaru ya ce a matsayinsa na baturen zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa a jihar Jigawa, ya tattara sakamakon zaben da jama'a suka kad'a, inda Buhari ya samu kuri'u 202,599, yawan adadin mambobin jam'iyyar da suka yi rejista da kad'a kuri'a a zaben, wanda ya nuna cewar gaba dayansu sun yarda Buhari ya zarce.
Ya ce: "Don haka a matsayina na mai tattara sakamakon zabe da kuma sanar da shi, na bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe wannam zabe ba tare da samun hamayya ba, kowa ya bi!"
Gwamnan ya jinjinawa shuwagabannin jam'iyyar da kuma mambobin kwamitin shirya zaben bisa namijin kokarinsu na ganin cewa an gudanar da zaben cikin nasara ba tare da samun wani cikas ba.
Da ya ke jawabi, shugaban kwamitin shirya zaben na jihar, Alhaji Umar Namadi, ya ce an gudanar da zaben bisa umurnin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na kasa.