Boko Haram ta kai wa sojojin Najeriya hari

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta na fafata wa da mayakan Boko Haram da suka kai musu hari a garin Damasak da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Wata sanarwa da kakakin rundunar Texas Chuku ya wallafa a shafin rundunar na Twitter ta ce 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin hari da misalin karfe shida na yamma.
A lokacin da ya wallafa sakon ya ce ana can ana fafatawa tsakanin sojojin da 'yan Boko Haram din da suka kai harin.
SHIGA WANNAN:Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su a 2019l
Ya kara da cewa sojojin na can suna sama da 'yan ta'adda, amma za a yi karin bayani nan gaba.
A baya bayannan dai mayakan Boko Haram na kara kaimi wajen kai wa dakarun Najeriya hari musamman a jihar Borno.
Harin na ranar Laraba shi ne na biyu da aka ba da rahoton Boko Haram ta kai wa sojojin Najeriya a cikin kasa da kwana bakwai.
Ko a karshen makon jiya ma 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin hari a garin Gudumbali a karamar hukumar Guzumala a jihar ta Borno, wanda Boko Haram ta ce ta kashe sojoji ta kuma kwaci makamai da motocin yaki.
To sai dai rundunar sojan Najeriya ta musanta ikirarin, inda ta fitar da wata sanarwa tana cewa sojojin da suka tarwatse sakamakon harin da aka kai musu sun sake haduwa wajen daya, sun kwace garin kuma ba a samu asarar rayuka ba.
Sojin Najeriya sun saki 'yaran Boko Haram' 183
'Rikicin makiyaya ya fi na Boko Haram illa'
Haka ma a farkon watan nan an ba da rahoton cewa 'yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya kusan 50 a wani hari da suka kai musu a garin Zari da ke karamar hukumar ta Guzamala.
Ko da ya ke a nan ma sojojin sun ce su ne suka tarwatsa 'yan Boko a harin sama da kasa bayan wasu bayanan sirri da suka samu.
Wasu masu sharhi dai na ganin karuwar hare-haren wani babban koma baya ne ga gwamnatin Najeriya da ke ikirarin ganin bayan Boko Haram.
Kuma masu wannan ra'ayi na ganin wajibi ne gwamnatin kasar ta kara zage damtse wajen yaki da kungiyar, saboda kar a koma gidan jiya.
A waje daya kuma irin wadannan hare-hare na sa wasu su ringa sanya alamar tambaya kan ikirarin da gwamnati ke yi na irin nasarar da ta ke cewa samu a yakin da ta ke yi da Boko Haram.