Online counter

Bashin Biliyan 20: Kungiyar ASUU ta karyata Gwamnatin Tarayya

Bashin Biliyan 20: Kungiyar ASUU ta karyata Gwamnatin Tarayya

LABARAI DAGA 24BLOG
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust ta kasar nan cewa Kungiyar nan ta ASUU ta Malaman Jami’an Najeriya ta karyata maganar cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko mata da makudan kudin da ta ke bi bashi kwanan nan.
Shugaban Kungiyar Malaman Jamu’an na Yankin Legas watau Farfesa Olusiji Sowande yayi karin haske game da labarin lokacin da ya zanta da ‘Yan jarida a tsakiyar makon nan. Sowande yace yaudarar Jama’a kurum Gwamnati ke yi.
Farfesa Sowande yace Gwamnatin Tarayya na kokarin gogawa Kungiyar ASUU bakin jini ne a idon jama’a don haka ta kawo maganar turawa Kungiyar Biliyan 20 a karshen bara. Shugaban na ASUU yace sam kudin bai zo hannun su ba.
Olusiji Sowande ya kara da cewa Gwamnati ta na ba Jami’o’i wannan kudi ne domin su amfana amma a hakikanin gaskiya ba ASUU ake turowa wannan kudi ba. Sowande yace yanzu haka ma dai ASUU na bin Gwamnati Biliyan 220.

Post a comment

0 Comments