Online counter

Barkonan Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago

Barkonan Aiki: Shugaban Ma'aikatan Buhari ya gana da 'Kungiyar 'Kwadago

LABARAI DAGA 24BLOG
Ko shakka ba bu ganawar ta gudana ne domin tattauna al'amurra tare da neman kawo sulhu dangane da fusatar kungiyar da ta yi sanadiyar shiga yajin aiki na gargadi gadan-gadan da a halin yanzu ta tsayar da kasar nan cik wuri guda.
Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa, ya kirayi wannan ganawa domin tabbatar da lamarin da ya kawo dakacin gudanar sulhu na neman cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar akan mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.
A yayin ganawarsa da shugabannin kungiyar ya fahimci cewa, rashin cimma matsaya da kayyade sabon mafin karancin albashin ma'aikatan kasar nan ya haddasa wannan lamari na yajin aikin kamar yadda Kyari ya bayyana.
yari ya fayyace matsayar gwamnatin tarayya kan lamarin da ya shafin mafi karancin albashin ma'aikata ga shugabbanin kungiyar yayin ganawarsu da shugabanta na kasa, Ayyuba Wabba ya jagoranci wakilanta zuwa fadar shugaban kasa.
Sai dai cikin kyautata zato da kuma sa rai kungiyar ta bayyana cewa, za ta tuntubi sauraran rassan ta na kasa domin zayyana ma su yadda ganawarta da shugaban ma'aikatan ta kasance, inda za ta bayar da ta cewarta dangane da ci gaban yajin aiki ko kuma ta janye.

Post a comment

0 Comments