Babu wanda ya isa ya hana ni yin takara — Dogara

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya ce ya soma gajiya da tsayawa takara amma zai sake tsayawa a zaben 2019.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga dumbun magoya bayansa daga jihar Bauchi wadanda suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja.
Dogara ya ce ba zai daina tsayawa zabe ba sai ya kammala ayyukan da yake yi na ci gaban Najeriya.
A cewar sa, ya sake tsayawa takara ne domin ya karya mutanen da suke so su yi masa ritaya.
'Yan majalisa 52 sun fice daga APC
KARANTA WANNAN:da-duminsa-gwamnan-apc-ya-amince-da
"Zan sake tsayawa takara ko don kada a ce an yi min ritaya," in ji kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriyar.
Yakubu Dogara, wanda dan jam'iyyar APC mai mulki ne, bai bayyana jam'iyyar da zai tsaya takara a karkashin ta ba.
Ya ce babu mutum daga jihar Lagos ko Bauchi da ya isa ya hana shi sake tsayawa takara.
Da alama ya bayyana hakan ne domin yin raddi ga gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar da jigon jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wadanda ake ganin ba sa jituwa tun da ya zama kakakin majalisar dokokin kasar.
Bola Tinubu dai bai ji dadin zaben Yakubu Dogara ba a kan kujerar kakakin majalisar dokokin tarayya, inda ya so a zabi yaronsa Femi Gbajabiamila.