Online counter

ASUU tace Gwamnati ta saba yarjejeniyar da aka yi Jami’o’i a 2017

ASUU tace Gwamnati ta saba yarjejeniyar da aka yi Jami’o’i a 2017

Yanzu haka dai Kungiyar ta fara kira gan Jami’a su tafi yajin aiki a fadin kasar nan. Shugaban Kungiyar na Yankin Filato Farfesa Lawan Abubakar ya nuna wannan lokacin da ya zanta da manema labarai jiya.
Yankin na Jos din ya kunshi Jami’o’in Abubakar Tafawa Balewa na Bauchi da Jami’ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe da ta Jos; da kuma Jami’ar Jihar Filato da ke Jihar Bokkos inji Shugaban na ASUU Lawan Abubakar.
Kungiyar ta kuma musanta cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko mata da Biliyan 20. Abubakar yace abin da Jami’o’in Najeriya 64 da ake da su su ke nema ya haura Tiriliyan guda don haka babu abin da Biliyan 20 za ma tayi masu.
A baya an yi wa Jami’o’i alkawarin Biliyan 220 kowace shekara. A dalilin hakane ASUU ta ke neman a ba ta Tiriliyan 1.1. Malaman Jami’ar sun nuna cewa ba su gamsu da tattaunawar da ake yi da Gwamnati na karin albashi ba.
Dazu kun ji cewa Shugaban ASUU na Yankin Legas watau Farfesa Olusiji Sowande yayi karin haske game da batun cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko mata da makudan kudin da ta ke bi bashi.

Post a comment

0 Comments