Online counter

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

-labarai daga 24blog 
A jiya, Alhamis, ne jam’iyyar APC tayi taron gangamin yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna a jihar Osun.
Jirgin dake dauke da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sauka a filin taron gagamin kamfen din jam’iyyar APC a birnin Osogbo na jihar Osun.
APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna

APC tayi taron ban mamaki a jihar Osun, hotuna
Taron APC a jihar Osun
Ana sanar da saukar jirgin Osinbajo da misalign karfe 4:05 na rana sai jama’ar dake wurin taron suka kaure da sowa da farinciki tare da nufar inda jirgin ya sauka.
Manyan ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka halarci taron sun yi tururuwa domin gaisawa da mataimakin shugaban kasar. Daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar da suka kewaye Osinbajo domin gaisawa da shi bayan ya sauka, akwai gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, shugabn masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran su.
Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da shugabanta na kasa, Adams oshiomhole, gwamnoni da sanatoci da mambobin majalisar wakilai sun halarci taron.

Post a comment

0 Comments