- labarai daga 24blog 
Jami'an tsaro a Kenya sun damke wani mutumin China mai suna Liu Jiaqi, saboda samunsa da furta kalaman nuna kyamar bakaken fata har ma da shugaban kasar Kenya cikin wata bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar Alhamis.
Hukumar kula da shige da fice da Kenya ta ce tuni an fara shirye-shiryen mayar da dan kasuwar zuwa 
"An soke takardan izinin aikinsa kuma za'a kore shi daga Kenya saboda samunsa da furta kalaman batanci ga jinsin Afirka," kamar yadda Hukumar shige da fice da Kenya ta rubuta a shafinta n
Bisa ga dukkan alamu Liu ya samu rashin jituwa ne tsakaninsa da wani ma'aikcinsa inda ya fara kwarara masa ashar ciki har da kalaman cin fuskan 'yan Afirka.
"Duk haka kuke, kamar birai, har ma da Uhuru Kenyatta. Dukkan ku haka kuke," inji Liu.
Bayan ma'aikatansa sun fada masa ya koma China idan yana ganin dukkan mutanen Kenya birai ne, dan kasuwan ya cigaba da kwarar ashar kamar haka.
"Ai dama nan ba garin mu bane, bana son kasar nan, dukkanku kaman birai ku ke. Bana son magana da ku saboda duk wari kuke, ga sakarci da talauci gashi kuma ku bakake ne. Bana son ku, mene yasa ba zaku kasance kamar Amurkawa ba?"
Ya da cewa yana zama a Kenya ne kawai saboda kudi na da muhimmanci a gareshi.
Wasu mutanen Kenya sun bukaci a gurfanar dashi gaban kotu ne ba kawai a mayar da shi kasar China ba. Wannan dai ba shine karo na farko da ake zargin 'yan China da nuna kiyaya ga bakaken fata a Kenya.