Online counter

An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya

An kama wani kasurgumin barawo a sanye da kakin sojoji a Najeriya

LABARAI DAGA 24BLOG 
Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Ogun dake a yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin kasurgumin barawo ne da kan sanya kayan sojoji tare da kwacewa jama'a kudaden su a Karamar hukumar Obafemi-Owode.
Barawon dai wanda aka ce shekarun sa kwata-kwata 23 an kama shi ne wajen karfe 8 na dare jim kadan bayan da ya kwatar wa wani tsohon soja mai suna Adeyemo Adegboyega Naira 86,000 a tsakiyar watan nan da muke ciki.
Tsohon sojan ne da hadin gwiwar jami'an 'yan sandan suka bibiyi sawun barawon har kuma suka kama shi inda dubun sa ta cika.
A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi babban burin sa idan har Allah ya sa ya lashe zaben shugaban kasar da za'a gudanar a shekara mai zuwa ta 2019 shine na ya tabbatar da ya bar wani babban abun azu a gani a sha'anin mulkin kasar nan.
Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da 'yan Najeriya mazauna kasashen Amurka da kuma Kanada a yayin ziyarar da yanzu haka ya ke kan yi a kasar ta Amurka, birnin New York.

Post a comment

0 Comments