Online counter

Amurka ta manta da sulhun ta da Koriya, an fara tsine-tsine daga Koriya

Amurka ta manta da sulhun ta da Koriya, an fara tsine-tsine daga Koriya

LABARAI DAGA 24BLOG 
A taron majalisar dinkin duniya dake gudana a Amurka a makon nan, kasar Koriya ta Arewa, wadda ke karkashin mulkin gurguzu na ilayan Kim Jong-Un shekaru kusan 60, wakilin kasar, Ri Yong Ho, wanda shine Ministan harkokin wajen kasar, ya koka kan takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar sa.
A cewarsa, Amurkar ita ke hana ci gaba da sulhun zaman kasashen biyu kan tebur, da karfafa takunkumai duk da sulhun da ake 
Ita dai Amurka ta yaki kasashen da ke bin gurguzu a shekarun baya, kuma ta raba koriyar biyu zuwa kudu da arewa, shekaru 60 da suka wuce.
An fara sulhu da Koriyar ta arewa mai fama da matsin tattalin arziki don ta hakura kar ta kera manyan makamai na kare daangi wadanda duniya ta hana amfani dasu.
Kasashe biyar ne kawai aka yarda su ajje makaman, Amurka, Chana, Rasha, Ingila da Faransa, kasashen da kuma ke kokarin nema a shekarun baya sun hada da Najeriya, Afirka ta Kudu, Libiya, Iraqi da Iran. Indiya, Pakistan da Israila tuni sun samu ta bayan fage.

Post a comment

0 Comments