Online counter

Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun gamsu a yi karashen zaben Osun


Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun gamsu a yi karashen zaben Osun

Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun nuna gamsuwarsu karashen zaben jihar Osun da aka gintse a Kudancin Najeriya.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da ofisoshin jakadancin kasashen suka fitar, sun bukaci a zauna lafiya kuma a je a yi zaben cikin kwanciyar hankali.
Kasashen dai na daga cikin hukumomin kasashen waje da suka sa ido a zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata.
Sun kuma yaba wa al'ummar jihar Osun da hukumar zabe ta kasar da kuma hukumomin tsaro kan rawar da suka taka wajen ganin an yi zaben lafiya na ranar Asabar lafiya.
Jawabin Obama yana sa dadin bacci - Trump
Kundin tsarin mulki ya halasta sake zaben Osun - Masana
Ba mu yarda da sakamakon zaben Osun ba —PDP
Sanarwar ta kara da yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a zaben da su bayar da goyon bayansu a yayin sake zaben a wasu kananan hukumomi.
"Muna jaddada muhimmancin kaucewa tashin hankali da rikici ko magudi yayin sake zaben.
"Duk wanda ya yi nasara a zaben da za a sake din to kar ya yi wa wanda ya fadi dagawa, shi kuma wanda ya fadi ya karbi hakan da kyakkyawar zuciya," a cewar sanarwar.
A korafe-korafen da suka yi game da sake zaben da INEC za ta yi, PDP da sauran manya-manyan jigata-jigatan, sun yi kira ga manyan kasahe duniya, kan yunkurin da suka ce APC ke yi na yi wa dimokradiyya zagon kasa.
A ranar Lahadi ne dai hukumar zabe ta INEC ta ayyana zaben gwamnan jihar Osun a matsayin wani zaben da ba a kammala ba.
Babban jami'in hukumar INEC a zaben farfesa, Adeola Fuwape, ya ayyana zaben a matsayin wanda ba a kammala ba ne don ratar da ke tsakanin 'yan takarar da ke kan gaba bai kai adadin kuri'un da aka soke ba.
An soke kuri'u 3,498 a zaben bisa dalilai na sace akwatin zabe da kuma batan-dabon jami'in hukumar INEC yayin da dan takarar jam'iyyar PDP ya fi dan takarar APC da kuri'u 353 kacal.
Daga baya INEC ta sanya ranar Alhamis a matsayin ranar da za a sake zaben gwamnan a wasu kananan hukumomi a jihar.

Post a comment

0 Comments