Online counter

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa a Kano

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa a Kano

- labarai daga 24blog
Tun kafin fara saukar ruwan sama hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) tayi has ashen za a samu ambaliyar ruwa a daminar bana. Sai dai hukumar ba ta fadi yankin da ambaliyar zata fi shafa ba.
A yanzu haka jihohin Najeriya, a kudu da arewa, na fuskantar annobar ambaliyar ruwa dake cigaba da haifar da asarar rayukan mutane, dabbobi da dumbin dukiya.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 10 yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye garuruwa da dama a kananan hukumomi 20 na jihar.
Sai dai wasu alkaluma da ba na gwamnati ba sun bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu yah aura 30.
Alhaji Aliyu Bashir, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ya ce bayan asarar rayukan mutane 10, ambaliyar rowan tayi awon gaba da dumbin dukiyar da yawanta ya kai biliyan daya.
Yanzu haka mazauna kauyukan da ambaliyar ta fi muni sun koma kwana a makarantun gwamnati tare da amfani da kwale-kwale domin fita ko shiga wasu kauyukan.

Post a comment

0 Comments