Online counter

Ambaliyar ruwa ta salwantar da 'ya'yan itatuwa na N25m a jihar KebbiAmbaliyar ruwa ta salwantar da 'ya'yan itatuwa na N25m a jihar Kebbi

Labarai daga 24blog 
Shugaban wannan kungiya, Alhaji Aminu Abubakar, shine ya bayyana hakan ga manema labarai cikin Birnin Kebbi a ranar Asabar ta yau da cewar rashin wadatattun magudanan ruwa ya haddasa aukuwar ambaliyar ruwa a babbar Kasuwar.
A sanadiyar haka shugaban kungiyar ke mika kokon barar sa ga gwamnatin jihar akan ta inganta gine-ginen wannan kasuwa domin gudanar da harkokin su cikin annashuwa gai da kwanciyar hankali tare da bunkasar hanyoyin samar da kudaden shiga ga g
Kazalika shugaban kungiyar ya kuma nemi gwamnatin jihar akan ta agaza da tallafi ga mambobin su da wannan annoba ta ambaliyar 
Yake cewa wannan tallafi zai taimaka kwarai da aniyya wajen bunkasa harkokin kasuwanci ga 'yan kasuwar ba tare da sun ji wani radadi na asarar da ta afka ma su ba.
Ya kara da cewa, kungiyar ta na da sama a mambobi 20, 000 cikin dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi da suke tallafawa gwamnatin wajen samar da abin yi ga fiye da matasa 3000 masu daukar dako da talla a fadin jihar.

Post a Comment

0 Comments