Online counter

Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su a 2019

Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su a 2019


-LABARAI DAGA 24BLOG
Yayin da zabukan gama-gari na shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, jama'ar kananan hukumomin Ukwa ta gabas da kuma ta Arewa dake a jihar Abia sun yi wa shugaba Buhari alkawarin ruwan kuri'un su a zabukan masu zuwa.
Majiyar mu ta ruwaito mana cewa al'ummar kananan hukumomin dai sun yi wannan alkawarin ne lokacin da tawagar wani masoyin shugaban kasar a jihar mai suna Ikechi Emenike ta kai masu ziyarar rangadi a karshen satin da ya gabata.
24blog ta samu haka zalika cewa al'ummar kananan hukumomin sun bayyana cewa tabbas shugaba Buhari din ya cancanci ya zarce a zaben mai zuwa idan akayi la'akari da irin cigaban da ya samarwa 'yan Najeriya.
A wani labarin kuma, Bangaren masana tattalin arzikin kasa watau Economist Intelligence Unit (EIU) na wata mujallar birnin Landan watau The Economist Magazine ta yi hasashen faduwar Shugaba Buhari zaben 2019 da za'a gudanar.
Mujallar dai wadda ake bugawa a birnin na Landan haka zalika tayi hasashen cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ce zata lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan watanni kadan.

Post a Comment

0 Comments