Online counter

Allah kare bala'i Ma'aikatan mai a Najeriya suna shirye shiryen tafiya yajin aikI

Allah kare bala'i Ma'aikatan mai a Najeriya suna shirye shiryen tafiya yajin aikI

-LABARAI DAGA 24BLOG
Yanzu haka an fara dar-dar a tsakanin 'yan Najeriya bayan da kungiyoyin ma'aikatan dake hada-hadar kasuwannin mai a Najeriya suka sanar da kudurin su na shiga yajin aiki na sai-baba-ta-gani.
Kamar yadda muka samu, kungiyoyin ma'aikatan man dai sunce za su shiga yajin aikin ne bisa dalilin muzgunawa da wasu daga cikin mambobin su ke fuskanta da wasu kamfunnan kasashen waje.
24blog ta samu cewa kungiyoyin na ma'aikatan man da suka hada da na man fetur da iskan gas watau Petroleum and Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENGASSAN) da Nigeria Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) sunce ana shirin korar mambobin su ne daga aiki.
Daga nan ne dai suka bukaci mahukunta da su shiga tsakani domin hana aukuwar hakan domin kuwa su da zarar hakan ta faru to suma kam za su shiga yajin aiki.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sanda a jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da basu san ko suwa ne ba sun sace wani dan siyasa da kuma wasu mutane shida a kauyen Nahuce dake a karamar hukumar Bungudu.
Yan sandan dai sun ce dan siyasar da aka sace tare da sauran mutanen shine Bello Dan Iya dake zaman tsohon Kansila na mazabar ta Nahuce da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Post a Comment

0 Comments