Online counter

ALAMOMI 5 da shugaba Buhari yayi magana kan su a majalisar dinkin duniya

ALAMOMI 5 da shugaba Buhari yayi magana kan su a majalisar dinkin duniya

LABARAI DAGA 24BLOG
Taron dai na kasashen duniya, kamar yadda muka samu majalisar dinkin duniya ce kan shirya shi a duk shekara inda akan tattauna akan al'amurran da suka shafi kasashe daban-daban. 
wannan shekarar ma, shugaban kasar ya halarci taron kuma ma a gabatar da jawabi a wajen ranar Talatar da ta gabata kuma ga wani tsakure da muka yi maku game da abubuwan da ya yi magaba akan su.
1. Ta'addanci
Buhari yayi magana kan yadda ta'addanci yake ta kara mamaye duniya da kuma irin kashe kashen da hakan ke jazawa a kasashe irin su Yamen, Siriya da ma Boko Haram. Ya kuma yi kira da a hadu domin kawo karshen hakan.
2. Rikicin makiyaya da manoma
Shugaban kasar ta Najeriya ya kuma yi magana akan yadda rikici tsakanin manoma da makiya yake ta kara yawaita a duniya tare da kira a kawo karshen matsalar.
3. Matsalar bakin haure
Shugaba Buhari ya kuma yi magana agame da matsalar bakin haure inda ya danganta lamarin da rashin kykkyawar rayuwa a wasu sassan duniya inda ya bukaci taimakon kasashe masu arziki don kawo karshen matsalar.
4. Yaki da cin hanci da rashawa
Haka zalika shugaban kasar yayi magana akan matsalar cin hanci da rashawa da yadda ta ke addabar kasashen Afrika da ma sauran kasashe masu tasowa.
5. Matsalar sauyin yanayi
A nan ma shugaban kasar yayi jawabi mai tsawo akan yadda ya kamata dukkan kasashe su maida hankali wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi dake matukar barazana ga al'umma.

Post a Comment

0 Comments