Online counter

Aisha Buhari tayi karin haske a kan rahoton sakin babbab dogarinta

Aisha Buhari tayi karin haske a kan rahoton sakin babbab dogarinta

LABARAI DAGA 24BLOG
Suleiman Haruna, darektan yaSa labarai a ofishin Aisha Buhari, ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar ta shafinsa na Tuwita a yau, Alhamis.
“Har yanzu jami’an tsaro na cigaba da binciken Baban-Inna a kan manyan laifukan cin amana da cin hanci day a aikata.
Zai yi wuya hukumar DSS ta sake shi ba tare da kamala bincike a kan dukkan tabargazar day a aikata ba,” kamar yadda yake cikin jawabin.
Tun a ranar Tallata ne Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta nesanta kanta daga rahotanni dake yawo a kafafen yada labarai cewar ta bayar da umarnin tsare sarkin dogaranta (ADC), Sani Baban-Inna, bisa zargin yin amfani da sunanta wajen karbar cin hancin biliyan N2.5 daga hannun ‘yan siyasa da jami'an gwamnati.
Sai dai Aisha ta bayyana rashin jin dadinta bisa yadda babban dogarin nata, mai mukamin Safuritanda na ‘yan sanda, ke amfani da mukaminsa da kuma kusancinsa da ita wajen zambatar mutane, musamman ‘yan siyasa da jami’an gwamnati.
Baban-Inna ya kasance babban dogarin Aisha tun shekarar 2016.
A jawabin da darektanta na yada labarai, Suleiman Haruna, ya fitar tun a ranar Talata, a Abuja, Aisha ta bayyana cewar kamun da jami’an tsaro suka yiwa Baban-Inna na cikin aikinsu da doka ta tanada.

Post a comment

0 Comments