Online counter

Aikin ganganci: Jami’an hukumar Kwastam sun bindige wani matashi a Katsina

Aikin ganganci: Jami’an hukumar Kwastam sun bindige wani matashi a Katsina

LABARAI DAGA 24BLOG
wannan lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba akan hanyar Dutsanma a kusa kwalejin ilimi na gwamnatin tarayya dake Katsina.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da faruwar lamarin a gabansa, inda yace matashin na tuka wata motace kirar J5, wanda da ita ake amfani wajen sumugal na shinkafa, sai dai da ya hangi jami’an kwastam sai yayi kokarin tserewa, daga nan su kuma sai suka bude masa wuta.
Jim kadan bayan faruwar lamarin, sai Yansanda suka inda aka yi kisa, inda suka dauke gawar matashin, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Gambo Isah ya tabbatar.
“Bayan mun samu labarin abinda ya faru ne muka isa wajen, da zuwanmu sai muka dauki mutumin muka garzaya da shi Asibiti, daga bisani likitocin asibitin suka tabbatar da mutuwarsa.” Inji DSP Gambo.
Idan za’a tuna a farkon hawansa mulki ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da kulle iyakokin Najeriya ga masu safarar shinkafa ta hanyar kasa, domin a samu a habbaka shinkafar cikin gida da manoman Najeriya ke nomawa.
Sai dai wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka ya janyo tsadar shinkafa sakamakon tashin gwauron zabi da farashin shinkafa ta yi tun daga shinkafar kasar waje har ta cikin gidan ma.

Post a comment

0 Comments