Online counter

2019: Saraki, Ribadu da Bafarawa sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan salon mulkin Buhari

2019: Saraki, Ribadu da Bafarawa sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan salon mulkin Buhari

-LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamna Sakoto, Alhaji Attahiru Bafarawa da tsohon Ciyaman din EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, duk sun bayyana ra'ayoyinsu game da kamun ludayin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Punch ta ruwaito cewa mutane ukun sun bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu kan yadda suke kallon salon mulkin shugaba Buhari a ranar Litinin 7 ga watan Satumba.i
24blog a gano cewa Ribadu ya yi hira da 'yan jarida a Abuja kuma ya ce ba zaiyi takarar shugabancin kasa ba saboda shugaba Buhari yana tafiyar da harkokin Najeriya yadda ya kamata.
A cewar Ribadu, yaki da rashawa abu shine aikin da ya fi kowanne wahala. "Sai an samu jarimi mai nagarta ne zai iya samun nasarar yaki da rashawa."
A bangarensa, Saraki ya ce shugaba Buhari yana mulkar al'ummar da kansu ya rabu. Shugaban majalisar ya fadi hakan ne a Abeokuta yayin da ya ke jawabi ga 'yan PDP na jihar Ogun.
Saraki ya ce Najeriya na bukatar shugaba da zai hada kan al'umma yadda kowa zai rike shi shugaba ba wanda kawai wani bangare na kasa ne kai son shi ba.
A yayin da ya ke magana a Akure ta jihar Ondo, Bafarawa ya ce gwamnatin APC ta lalata tattali arzikin Najeriya.
Ya ce, "Idan muka karbi mulki, zamu mayar da hankali wajen gyarar mu'ammala tsakanin bangarorin 'yan Najeriya. Zamu gyara kurakuren da akayi a baya."

Post a Comment

0 Comments