Online counter

2019: Samuel Ortom ya yanki Tikitin takara ta kujerar Gwamnan jihar Benuwe

2019: Samuel Ortom ya yanki Tikitin takara ta kujerar Gwamnan jihar Benuwe

Labarai daga 24blog
Kakakin fadar gwamnatin jihar, Terver Akase, shine ya bayyana hakan yayin da gwamnan ya yanki tikitin sakamakon ci gaba da karatowar zaben fidda gwani na jam'iyyar.
Gwamnan ya mika godiyar sa ga shugabanci da kuma mambobin jam'iyyar dangane da ba shi dama ta yankar tikitin jam'iyyar domin fafafatawa a babban zabe na 2019.
Ya kuma yabawa magoya bayan sa na jihar tare da gargadin su akan ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin su gami da kawar da gaba da kiyayya ta bambance-bambancen akidu na siyasa.
Kazalika gwamnan ya kuma mika godiyar sa ga al'ummar jihar sakamakon kwarara addu'o'i da fata na gari a garesa, inda ya sha alwashin ba zai kunyata su ba.

Post a Comment

0 Comments