Online counter

2019: Matasa 7000 zasu yi karo-karo don saya wa tsohon gwamna fom din takara

2019: Matasa 7000 zasu yi karo-karo don saya wa tsohon gwamna fom din takara

- labarai daga 24blog
Mun samu daga Daily Trust cewa matasan Najeriya 7000 sun dau alwashin yin karo-karon N1,000 kowannensu don saya wa tsohon gwamnan jihar Abia, Dr Orji Uzor Kalu, fom din takarar zaben Sanata na yankin Abia ta Arewa a zaben 2019.
Matasan da ke suka dau waje guda karkashin kungiyar O.U.K sun bayyana Kalu a matsayin shugaba mai nagarta da ya kirkiri ayyuka da dama hakan yasa suke son ya tafi majalisar dattawa ya cigaba da ayyukan alkhairin kamar yadda mai magana da yawun Kalu ya ce.
Sanarwan ta kuma ce, matasan sunyi amanna cewa Kalu zai iya sayan fom din da kansa amma za su saya masa ne saboda su nuna godiya bisa abubuwan alkhairi da ya yi a jiharsa. Matasan sunce za su mara masa baya har sai sunga abinda ke ture wa buzu nadi.
A yayin da yake managa da manema labarai game da yakin neman zaben, Sakatare na kasa na O.U.K, Emeka Anyalekwa ya yi bayyanin cewa tafiyar na matasan mai taken #700Youth4OUK ba tafiya na samun kudi bane.
Tafiya ce ta nuna kauna saboda amince da kauna da su ke yiwa Orji Uzor Kalu (OUK). "OUK ya tallafa mana a fanoni daban-daban na rayuwarmu kamar bayar da ilimi kyauta, samar da ayyukan yi, tallafin guraben karo karatu da sauransu.
"Akwai sama da matasa 10,000 a Najeriya da Dr. Orji Kalu ya samarwa ayyukan yi da wasu sama da 100,000 da ke dogaro da wanda ke masa aiki domin tafiyar da rayurwasu." inji Emeka.
Sakataren ya ce Kalu ya gina masana'antu da yawa kuma yana cigaba da ginawa saboda matasa su samu ayyukan yi. Ya yi ikirarin cewa babu wani dan siyasa da ke samarwa matasa aiki kamar Kalu.

Post a Comment

0 Comments