Online counter

2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna

2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna

LABARAI DAGA 24BLOG
Kwamitin gudanarwan na jam'iyyar ne ta dauki wannan matakin sakamakon rahoton da da samu daga kwamitin tantance 'yan takarar gwamna na jam'iyyar.
Mrs Aisha, wadda aka fi sani da Mama Taraba tana son takarar kujerar gwamna na jihar Taraba ne yayin da Mr Shittu Adebayo shi kuma yana niyyar takarar gwamna ne a jihar Osun.
Duk da cewa kwamitin ta soke takarar Mr Shittu ne saboda bashi da shaidar kammala NYSC ko kuma hidimar kasa, kwamitin ba ta bayar da dalilin ta na soke takarar Mrs Alhassan ba.
Wasu masu neman takarar gwamnan da kwamitin bata tantance sun hada da Osiobe Eric Okotie (Delta), Ejikeme Ugwu (Enugu), Ibrahim Mohammed Mera (Kebbi), Danladi Envulu-Anza Halilu (Nasarawa) da Abubakar Mamma Jiya Maaji (Niger).

Post a comment

0 Comments