Online counter

Zaman Aure: Jan hankali ga sabuwar amarya

Zaman Aure: Jan hankali ga sabuwar amarya

Zaman auren kusan ya fi kowanne zama dadi, haka kuma ya fi komi wuya, domin Hausawa ma suna fadar zo-mu-zauna-zo-mu-saba!
Aure idan zamansa ya yi dadi za ka ga ana jin dadi, ana sam barka tsakanin amarya da ango da mahaifan ango da mahaifan amarya. Har ma ana gasa wurin kyautata wa kowane bangare, kowa zai rika kokarin ganin ya kyautata wa wani bangare domin nuna masa jin dadinsa da godiya a kan diyaucin da aka nuna masa.
A wannan lokacin za ka sami ango yana wani haske, yana ciccika, yana kasaita tamkar wani basarake, ko wata agwagwa. Yayin da ita kuma amarya za ka ga tana sheki da wani irin kumbura tamkar kazar Turawa. Haka za ka ga tana wani irin annuri da sakin fuska. A wannan lokacin ko iska ta kada sai ta yi masa dariya, to, balantana wani ya yi mata magana ta wasa ko ta zolaya. Shi ango kada ma ka tona bangarensa, domin shi kam wannan zarafin ya koma wani dan karamin tauraro ko kuma ya koma tamkar mota kirar sabuwar shekara.
AssalamuAlaikum?
Wa’alaikus-salam!
Barka da wuni?
Barkadai!
Kai jiya na hadu da Ibrahim yayan Suwaiba!
Masha Allahu! To, ya gane ka kuwa?
Eh! kwarai kuwa ya gane ni sossai.
Kai amma wadannan bayin Allah suna da  kirki.
Wallahi haka ne, kuma dattijai.
Ai wani ya gaya mani cewa, idan mutum ya sami suruki kamar Alhaji Abdullhamid, hakika ya yi arziki.
Muhammad, wannan ita ce dalilin da ya sanya iyayenmu ke ba mu shawara, idan za mu yi aure a kan mu auri ’yar dattijai.
Wannan tana daya daga cikin hirar da za ka ji ana yi daga bangaren ango, idan suka hadu da wani daga ’yan uwan amarya. Wanda kuma hakan ne zai faru idan ana hira a bangaren ’yan uwan amaryar idan sun hadu da na angon.
Yayin da su kuma abokan ango za su dinga zolayar ango a kan cewa, wallahi wane ka canza, ka yi kiba, ka koma dan lukuti da kai. Abu sai ka ce agwagwa. Ko kuma wani ya ce da ango wallahi wane ban zaci cewa za ka yi kiba ba, amma kuma yanzu sai ga shi ka yi kiba, ka yi fari, ka yi haske da kyal-kyali, kai amma Suwaiba ta iya kiwo. Duk wadannan su suke nuna cewar aure ya yi kyau, an samu zaman lafiya kamar yadda ake so da buri.
To, amma idan aure bai yi kyau ba, zaman lafiya bai samu ba, to, wannan ba sai na yi bayani ba; domin duk abubuwan da na zayyano a baya, to, sabaninsu ne zai auku. Idan an hadu za a rika cin mutuncin juna da yi wa juna muggan kalamai da habaici, wani lokaci har da zagi. A wannan lokacin amarya za ta koma tamkar kazar da kurdumu ya kama, ko itaciyar da tsawa ta fado a kanta.
Ango kuwa kada ka so ganinsa a lokacin, domin ya koma tamkar akuyar mayya, ko tamkar wanda yake da sabon hauka, kowa yana nesa-nesa da shi, to, balantana wani ya yi masa maganar fara’a ko zolaya idan dai ba wanda ke son cin zarafinsa ba ko idan dama shi makiyinsa ne.
To, wai duk mene ne ke kawo hakan? Zaman lafiya da rashin zaman lafiya. Wasu sukan dora alhakin abin kawai a bangaren mata, ko kuma bangaren iyayen ango. To, amma dai ni zan dora alhakin duk wani abu da ya faru a zamantakewar su haujin mata da mijin, wani lokacin ma namijin ya fi laifi a wannan bangaren amma dai laifi kowa da irin nasa.
Mafita: Bayan an yi aure an gama biki da karbar gaisuwar ’yan uwa na nesa da na kusa, wadanda ke zuwa domin yin addu’a da sanya albarka. Kowa zai watse, za a bar mutum biyu da abu biyu. Su ne amarya sai ango sai kuma halayen amarya  da halayen ango. To, a wannan lokacin ya kamata idan son samu ne, ango zai zauna da amarya su fuskanci juna. Ta wannan wurin za su tattauna a kan muhimman abubuwan da za su kawo musu jin dadi da albarka a zamantakewarsu. Kuma a nan ango ne ya kamata ya yi wa amarya wa’azi a kan ta ji tsoron Allah a kan zamantakewar aure.
A nan angon yana iya ya dan gutsura wa amarya wani abu daga sirrin rayuwarsa na yadda yake son amaryar ta kasance da yadda yake son ta yi ma’amala da shi da mahaifansa da sauran ’yan uwansa da sauran jama’a. Kuma zai iya dan bayyana mata wasu daga ’yan ka’idojinsa ko abubuwan da yake so. Haka babu laifi idan ya tambaye ta a kan abubuwan da take so, ko kuma abubuwan da ba ta so. Idan an bi wannan hanyar, in sha Allahu abubuwan za su tafi cikin tsari, da kuma samun salama da zama mai inganci tsakanin ango da marya.
Sai dai kuma koda an sami matsala alhali kuma duk an zauna an tsara abubuwan da ya kamata a yi, to, ko shi bai kamata a yi harkar dabbobi ba wajen warware matsalolin ko ganin cewa kowa ya ji a jikinsa. A’a shi ma akwai matakan da ya kamata ma’aurata su bi domin ganin an sami maslaha da zaman salama  ta wannan bangaren.
Idan ana samun matsala tsakanin ango, ko tsakanin mahaifan ango wadanda su ne watakila za ki zauna da su, to amarya, za ki zauna ki yi duba da nazari a kan abin da ya kawo ki, wato zaman aure ne za ki yi, za ki zauna da wanda ba ki taba rayuwa ta wuni daya da shi ba, yau shi za ki zauna karkashinsa. Yakan yiwu tauraruwarku ma ba daya ba ce, ke ra’ayinki daban ra’ayinsa daban to, a nan ya kamata ke ki ajiye ra’ayinki, ki kulle shi cikin zane, ki boye shi, sai ki rungumi ra’ayi da dabi’un mijinki, wanda ta wannan hanyar idan har halayen ba kyawawa ba ne; za ki iya ki canza masa su daga baya amma kuma sai kin nuna goyon bayansa sa’annan zai saurare ki har ya fahimci nasiharki.
Amarya ta dubi tarbiyya da ilimin da aka koyar da ita daga makaranta da kuma daga iyayenta da masu yi mata tarbiyya, duk ta tara wadannan abubuwan ta biya adashinsu. Ma’ana, yanzu ne za ta biya mahaifanta adashin da suka zuba mata na tarbiyyar da suka yi mata. Kuma a nan za ta biya malamin da ya koyar da ita addini da sauran al’amurran duniya.
Idan har zaluntarki ake yi daga bangaren miji ko mahaifansa ko ’yan uwansa to, kada ma ki kai karar su wajen mahaifanki, a’a zauna da su ki ci gaba da kyautatawa a gare su da yi musu abin da duk kika san zai kyautata rayuwarsu ko da ba su yaba miki. A’a, shi Allah da kike yi dominSa yana nan yana ganin ki, yana yaba miki kuma yana ba ki lada kuma ko-ba-jima-ko-ba-dade sai Allah Ya nuna gaskiya tsakaninku kuma Allah Ya sanya soyayya da fahimtar juna tsakaninku.
Hausawa dai sun ce, komai ya baci hakuri ne babu! Ni kuma zan ce,  komai ya baci maganinsa Allah!
Inaga kafin mu shiga cikin gidan aure, zaiyi kyau mu fara gabatar da wasu shawarware ga ‘yan’uwa, wa’danda zasu taimaka matuka wajan rage matsalolin dake faruwa a gidajan auranmu.
Kasancewata mace zan fara da gabatar da shawarar dana samo daga wajan Malamina (Mal Umar Ya’akub) ga ‘yan’uwana mata….

Post a comment

0 Comments