Yaya rayuwa take kafin zuwan Google?

Daga Roland Hughes
BBC News

Me ke maganin ciwon sanyi? Wacce kasa ce tafi yawan jama'a a duniya? Me ake nufi da so? Wa ya kirkiri jirgin sama?
Tun kafa shi shekaru 20 da suka gabata, Google ya kasance kundin bincike da ke amsa tambayoyi kai-tsaye a intanet cikin sauki. Ya zama aikatau inda a ranar Laraba aka ci shi tarar dala biliyan biyar kan gwagwarmayarsa da abokan hamayya.
An rasa ayyuka da dama da suka shafi bincike bayan kirkiro da Google, har ya kasance yanzu an manta da yadda ake gudanar da ayyukan bincike.
Dan jarida
Gareth Hughes tsohon dan jarida ne da ya yi aiki da jaridar Daily Post a arewacin Wales tsakanin 1974 zuwa 2006 (shi ne mahaifin wanda ya rubuta wannan makala).
"Na kan yi rubutu game da irin abubuwan da babu wanda zai yi tunanin nasan komai," in ji shi. "Ina da kundin litattafai da dakin karatu, amma abu mafi muhimmi shi ne tabbatar da gaskiya."
Muna da kuma dakin karatu a ofishinmu da ke Liverpool inda muke ajiye dukkanin jaridu da duk wani labari.
"Idan kana neman wani abu kan wani batu, jami'an da ke kula da dakin karatu za su bincika kuma su gabatar da shi a gareka. Aikinsu yana da ban sha'awa."
"Ni ma na rika ajiye komai - na tuna da labarin wata jaririya da aka haifa can wani waje mai nisa kuma a tsakiyar hunturu, kuma nauyinta bai wuce kullin suga ba. An lullube ta da auduga a cikin wata motar daukar marar lafiya a yayin da sannu a hankali ake tafe da ita zuwa asibiti, kuma ta rayu cikin yanayi na zubar dusar kankara, a cikin wani lamarin da ba a taba tunanin za ta yi rai ba.
Na rubuta labarin watanni shida bayan ta bar asibiti, daga baya kuma ina cikin binciken abubuwan da suka faru sai na ci karo da labarinta. Sai na lura cewa ta kusa cika shekar 21 da haihuwa, saboda haka sai na fara neman inda take. kuma sai na gane cewa tana zaune a kusa da ofishina ne."
"Zuwan Google ya taimaka kwarai, amma babu abin da yafi yin bincike da kanka dadi".
Na kiyaye duk abin da ya faru - ina tunawa da labarin game da jaririn da aka haife mil daga ko'ina cikin tsakiyar hunturu, nauyin jakar sukari. An saka shi a cikin gashi na auduga a cikin motar motar asibiti ta hanyar tafiya ta hankali da dusar ƙanƙara da kankara a fadin mahaifa, kuma ba a sa ran ta tsira.
The barrister
Hilary Heilbron QC ta fara aiki a matsayin karamin lauya a shekarar 1972. Yanzu ta zama mambar wani babban ofishin lauyoyi a Landan, kuma ta dade tana aikin shari'a.
"A matsayina na karamar lauya, akan ba ni umarni kuma dole ne in yi cikakken bincike akai - kamar kundin shari'a. da litattafai - har zuwa dakin karatu. Domin yin sauran bincike kuwa, dole nake zuwa bababn dakin karatun lauya na Middle Temple domin samun bayanin wata shari'ar da ke da alaka da wata shari'ar."
"A yanzu kuwa dukkan bayanan shari'a na cikin intanet - kaga ina da jerin littatafan shari'a a kantar ofishina, amma basu da wani amfani a greni sai dai na ado."
"Kuma babu damar yin tallace-tallace a wancan lokacin, saboda haka dukkan maganar kasuwanci da ake yi a yanzu bai ma taso ba. Kana yin aikinka ne yadda ya kamata, kuma sai kayi fatan wadanda kayi ma aikin za su ji dadi su kuma dawo."
Mai lura da dakin karatu
A shekarun baya, ma'aikata a bababn dakin karatu na birnin New York sun zama tamkar manhajar Google mai jini, domin sun rika karbar tambayoyi daga mutane kuma su kan ba su amsoshin tambayoyin.
Amma a 'yan shekarun nan, ma'aikatan sun gano wani tsohon akwati cike da irin tambayoyin da jama'a suka yi masu a da. Sai suka saka su a shafinsu na Instagram.
Wani ya tambayesu a 1948: "Ina zan iya samun ciakakkun bayanai akan dukkan ciniki da kudaden da su kayi musayar hannu a kasuwancin gawawwaki?"
A 2018 Google ya yi nuni kan wannan binciken da Reuters suka yi kan cinikin gawa a Amurka .
Wani kuma ya tambayesu a 1949, "Shin beraye na yin amai?"
An amsa masa cewa lallai beraye na yin amai.
"Idan maciji mai guba ya sari kansa, gubar za ta kashe shi?"
Da alama mutane na da tambayoyi masu sarkakiya a 1949. Amma har zuwa 2018 Google ya ce: babu wanda ya sani har yanzu.
"Wane lokaci ne tsakar rana?"
Amsar ita ce Karfe goma sha biyun rana.
The academic
Janice Yellin ta kammala karatun digirinta na uku wato PhD a fagen nazarin tarihin al'ummar Nubiya a kwalejin Brandeis da ke birnin Bostaon a farkon shekarar 1970. A yanzu ta zama farfesa a bangaren tarihi a kwalejein Babson da ke Massachusetts.
Ta ce "Google ya sauya komai. A yanzu ba sai na tafi wani dakin karatu ba domin neman wani bayani. Ina samin saukin bincike na kimanin kashi 80 cikin 100.