Shugaba Buhari ya zaburar da mata kan shiga siyasa domin a dama da su 

A yau Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya zaburar da matan Najeriya kan cewa zu fito kwansu da kwarkwata a dama da su cikin harkokin siyasar Najeriya saboda su samu damar kawo canjin da ake bukata a kasar. Shugaban kasar ya yi wannan kirar ne a wajen taron mata masu neman kujerun siyasa wadda Cibiyar kungiyoyin mata na kasa (NCWS) ta gudanar a Abuja. Shugaba Buhari kuma ya ce yana kyautata zaton matan Najeriya za su fito su jefa masa kuri'a a zaben 2019 kamar yadda su bashi goyon baya a zaben shekarar 2015. Shugaba Buhari ya zaburar da mata kan shiga a dama da su a siyasa Source: Facebook Ya ce mata sune suke da kashi fiye da 50% na masu kada kuri'a a Najeriya kuma tarihi ya nuna cewa mata sunfi kwazo da rikon gaskiya fiye da takwarorinsu maza idan suka samu mukamai.

tuggun da tsohon maigidan nasa ke kulla masa Ya kara da cewa, "'Yan siyasa suna dogaro da mata sosai saboda suna rike alkwari sosai muddin suka amince da dan takara hakan yasa 'yan siyasa ke kokarin ganin mata sun amince da su. "Hakan yasa na ke so mika godiya ta ga matan Najeriya ta yadda suka bani goyon baya a zaben shekarar 2015. Ina fatan za su cigaba da bani goyon bayan musamman yadda naga dandazon taron mata da suka taru a nan." Shugaban kasan ya ce Najeriya kasa ce mai dimbin albarka da mutane masu basira da kwazo kuma muddin aka samu shugabanci nagari, kasar za ta bunkasa sosai ta zama abin kwatance. Shugaba Buhari ya ce ya gana da 'yan majalisa mata inda suka gabatar masa da batun dokar dai-daiton samun aiki tsakanin jinsi (wato maza da mata) da ke gaban majalisa da wasu dokokin. Shugaba Buhari ya ce yana goyon bayan dokar saboda hakan zai kara bawa mata damar shigowa gwamnati da siyasa.