RANAKUN BIKIN SALLA.

Wannan lokaci ne na musamman, rana ce ta farin-ciki ga dukkan masoya. Ranakun bikin salla, lokuta ne da kasantuwata a tare da ke ka iya kai wa ga sanadin ‘karuwar yalwatuwar murmushin fuskata. Rashin kasancewarmu a tare a cikin wannan rana ya haifar min da damuwa a zuciyata, amma duk da haka ba zan gaza ba wajen furta miki cewa, Ina Son Ki. Barka Da Salla.