Online counter

Rabin 'yan Najeriya na fuskantar rashin adalci daga Shugaba Buhari

Rabin 'yan Najeriya na fuskantar rashin adalci daga Shugaba Buhari

Hukumar makarantar koyar daa harkokin gudanarwa ta kasa watau Nigerian Institute of Management ta ce rabin 'yan kasar na fuskantar wariya da rashin adalci daga shugaba Buhari tun da ya hau mulki.
Hukumar dai ta cewa hakan na faruwa ne kuma saboda kin nada mata da ke zaman rabin 'yan Najeriya da yayi a cikin gwamnatin sa a madafun iko tun bayan darewar sa kan karagar mulki a shekarar 2015.
"Rabin 'yan Najeriya na fuskantar rashin adalci daga Shugaba Buhari"
"Rabin 'yan Najeriya na fuskantar rashin adalci daga Shugaba Buhari"
24blog.com.ng ta samu cewa shugaban makarantar kuma shehin malami Farfesa Olukunle Iyanda yace a gwamnatin da ta shude ta Jonathan ya baiwa mata kaso 33 cikin 100 amma Shugaba Buhari kaso 10 kacal ya ba matan.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ebonyi dake a kudancin Najeriya kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP da kuma ke mulki a jihar mai suna Dabid Umahi, mun samu labarin cewa ya hana 'yan jam'iyya mai mulki a matakin tarayya yin anfani da babban filin wasan jihar wajen yin taro.
Sai dai da yake karin haske game da dalilin yin hakan, mai magana da yawun sa Cif Emmanuel Uzor ya bayyanawa 'yan jarida cewar ana aikin gyare-gyare ne ga filin wasan.

Post a Comment

0 Comments