PDP za ta kalubalanci sakamakon zaben Katsina

Babbar jam`iyyar adawar Najeriya, PDP, ta ce za ta kalubalanci sakamakon zaben cike-gurbi na kujerar dan majalisar dattawa ta mazabar Katsina ta Arewa, inda ta sha kaye a hannun jam`iyyar APC mai mulkin kasar.
Jam'iyyar APC dai ta yi nasara ne a zaben da wa da kani suka yi takara inda APC ta samu kuri'u 224,607, ita kuwa PDP ta samu 59,724.
Duk da irin tazarar da sakamakon zaben ya nuna cewar APC ta bai wa PDP, jam'iyyar PDP ta ce ba ta yarda ba domin tana ganin an yi magudi.
Sai dai kuma, jam'iyyar APC ta musanta zargin, tana mai cewa shure-shure PDP din ke yi kawai.
Kani ya doke yayansa a zaben cike gurbi na Daura
APC ta lashe zaben dan majalisa a Kogi
Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Majigiri kuma ya shaida wa wakilin BBC Ibrahim isa cewa ba su amince da sakamakon zaben ba.
"Gaba daya mun yi watsi da sakamakon wannan zabe. Ba mu taba samun lokacin da ake sayen kuri'a da kudi ba irin wannan lokacin. Tamkar sakamakon nan a rubuce yake, karanta shi ake yi. Yaya za a yi a ce cikin mazabu 128 a yankin Daura in banda mazabata babu inda PDP ta ci zabe?" Inji Alhaji Salisu
Ya kara da cewa "A shirye muke za mu wuce kotu da yardar Allah."
Sai dai kuma jam'iyyar APC ta ce mazabar Katsina ta arewa mazaba ce da APC ta yi kaka-gida kasancewarta mazabar Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Kakakin jam'iyyar APC na jihar, Abubakar Gambo Danmusa, ya shaida wa BBC cewa tun daga shekarar 2003 da Buhari ya shiga siyasa, jam'iyyarsa ce ke cin zabe a yankin.
Zabukan cike-gurbi na kujerun `yan majalisar dattawa biyu da dan majalisar wakilai daya da kuma dan majalisar dokokin jiha daya aka yi a Najeriyar a ranar Asabar din da ta gabata, amma kujera dan majalisar jiha kadai jam`iyyar PDP ta tsira da ita, wadda aka yi a jihar Cross-River da ke kudu-maso kudancin kasar. Sauran kuwa duka APC ce ta lashe su.