PDP ta rusa shugabanninta na Kano

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta rusa shuganninta na jihar Kano, inda ta maye gurbinsu da kwamitin rikon kwarya.
Kwamitin kolin jam'iyyar ne ya dauki matakin a wani taro da ya yi a ranar Alhamis.
Wata sanarwa da kakakin PDP na kasa Kola Ologbondiyan ya sanyawa hannu ta ce an rushe shugabancin ne nan take.
Sanarwar ba ta yi bayani ba kan dalilan da suka sanya aka rushe shugabancin jam'iyyar na Kano ba.
To sai dai wasu bayanai sun nuna cewa matakin wani yunkuri ne na mikawa Sanata Kwankwaso shugabancin jam'iyyar a Kano.
Wani makusancin jigo a jam'iyyar a Kano Malam Ibrahim Shekarau, Malam Gali Sadik ya shaida wa BBC cewa matakin uwar jam'iyyar ya jefa PDP a Kano cikin rudani.
Ya ce dama tun lokacin da Sanata Kwankwaso ya shiga jam'iyyar aka fara samun rikici, kan yunkurin kwace shugabancin jam'iyyar a jihar.
Kwankwaso ya kaddamar da takararsa a zaben 2019
Da gaske an yi wa Kwankwasiyya tawaye a Kano?
Ya kara da cewa tuni shugabannin jam'iyyar na Kano suka samu umarnin kotu da ya hana rushe shugabancin jam'iyyar a Kano.
A baya ma an samu irin wannan matsala lokacin da Kwankwaso ya koma APC, abinda ya sa Malam Ibrahim Shekarau da magoyansa suka fice saboda zargin rashin adalci daga shugabannin APC na kasa a lokacin.
A yanzu haka dai bayanai na cewa jagororin jam'iyyar na Kano da suka hada da Malam Ibrahim Shekarau da Ambasada Aminu Wali da kuma Sanata Bello Hayatu Gwarzo sun yi tsayuwar daka cewa ba za su bari a kwace jam'iyyar a mika wa Kwankwaso ba.
Hakan dai na iya zama wani babban kalubale ga jam'iyyar, da zai iya rage mata tagomashi a jihar.