Mece ce makomar Pogba da Karius da Rabiot da Mario da Norwood da kuma Bakayoko?

AC Milan tana hakon dan wasan
Chelseadan kasar Faransa mai shekara 23, Tiemoue Bakayoko, domin ya buga wasan aro, wanda zai zama kwantiragi na din-din-din, in ji (Sun).
Barcelona za ta nemi Paul Pogba bayan an rufe kasuwar musyaar 'yan wasa ta Turai ranar 31 ga watan Agusta, bayan ta "amince a asirce" cewar Manchester United ba za ta sayar da dan wasan Faransan mai shekara 25 ba a cikin wannan watan, in ji (Telegraph) .
Golan Liverpool Loris Karius, mai shekara 25, dan wasa ne da Besiktas ke hako. Kungiyar ta Turkiyya tana son dan kasar Jamus din ya buga mata wasan aro a tsawon kaka daya, in ji (Sun).
Kawo yanzu dai dan wasan Ingila, Raheem Sterling, bai yarda ya tsawaita kwantiraginsa ba da Manchester City ba, yayin da kocin kungiyar Raheem Sterling ya ce kungiyar "tana jin dadinsa kuma za ta so Raheem ya tsaya", in ji (Telegraph).
Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya ce dan wasan baya David Luiz yana da "babbar makoma" a kulob din , duk da cewa dan kasar Barazil din mai shekara 31 ba ya samun gurbin wasa sosai karkashin tsohon kocin kulob din Antonio Conte, in ji (Mirror).
Sarri ya ce ya yi nadamar rashin saya wa
Chelsea Gonzalo Higuain, amma dan kasar Argentina din mai shekara 30 ya ce ya koma AC Milan ne daga Juventus domin Sarri "kadai ne yake so na a Chelsea" amma kuma "a Milan kowa na so na", in ji Star
Dan wasan tsakiyar Tottenham dan kasar Ingila Dele Alli ya ce ababen da ke tafiya a kulob din ba su yi tasiri kan 'yan wasan ba bayan Spurs ba ta sayi ko dan wasa daya ba a kasuwar musayar 'yan wasan lokacin bazara da aka rufe kwanan nan, in ji (Mail).
Dan wasan bayan Manchester City mai shekara 23 Jason Denayer ya ki ya je ya buga wasan aro domin dan wasan bayan Belgium din yana son ya koma kungiyar kwallon kafar Turkiyya, Galatasaray, in ji
(Star) .
Keftin din Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bukaci Juventus ta nemi dan wasan tsakiyar Lazio Sergej Milinkovic-Savic. An alakanta dan wasan mai shekara 23 dan kasar Serbiya da komawa Manchester United da Chelsea, in ji (Star) .
Dan wasan tsakiyar Paris St-Germain Adrien Rabiot, mai shekara 23, ya ki tayin tsawaita kwatiraginsa da zakarun gasar Ligue 1. Kwantiragin dan wasan Faransan zai kare a karshen wannan kakar ,in ji
(L'Equipe - in French) .
Dan wasan bayan Schalke dan kasar Jamus Thilo Kehrer, mai shekara 21, ya shirya domin komawa Paris St-Germain bayan an cimma yarjejeniyar fan miliyan 33, in ji (Guardian) .
Real Betis za ta iya tayin sayen dan wasan kungiyar Inter Milan, Joao Mario. Dan wasa tsakiyar Portugal din, mai shekara 25 ya buga wasanni 14 a lokacin da ya je buga wasan aro a West Ham United a kakar da ta gabata da gasar kofin duniya, in ji (Mundo Deportivo) .
Dan wasan tsakiyar Watford dan kasar Faransa Abdoulaye Doucoure, mai shekara 25, ya nuna cewar zai bar kulob din a gaba, in ji (Watford Observer).
Rahotanni sun ce Manchester United na tattaunawa da Fenerbahce kan dan wasan bayan Argentina mai shekara 28, Marcos Rojo, in ji (Mirror).