Mece ce makomar Mourinho da Mbappe da kuma Rakitic?

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya shaida wa abokansa cewa da a wani kulob yake da yanzu ya yi tafiyarsa.
An ce dan kasar Portugal din yana fuskantar takaici game da irin rashin kulawar da yake fuskanta daga mataimakin shugaban kulob din Ed Woodward, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.
Ita ma Manchester Evening News ta ruwaito cewa duk da takaicin da yake ji, har yanzu Mourinho yana son ci gaba da zama a kulob din.
Har ila yau (Mail) ta ruwaito cewa tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane yana son aiki a Manchester United idan Mourinho ya tafi.
Jaridar (Sun ) ta ce Mourinho zai samu tallafi a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu, yayin da United take zawarcin dan wasan bayan
Tottenham Belgium Toby Alderweireld, mai shekara 29.
Paris St-Germain tana neman dan wasan
Spurs Danny Rose , kuma kulob din yana son ya sayi dan wasan Ingila, mai shekara 28, kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta Turai, in ji (Mirror).
(Marca ) tana cewa Real Madrid har yanzu tana neman wanda za ta saya domin maye gurbin Cristiano Ronaldo kuma suna ganin za su sayi dan wasan gaban Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekara 19.
Kungiyar ta Spain a halin yanzu tana ganin "abu mai matukar wuya ne" ta sayi daya daga cikin manyan 'yan wasan gaban gasar Firimiya a wannan kasuwar saye da musayar 'yan wasan, kuma sun mayar da hankali kan dan wasan gaban Valencia Rodrigo, mai shekara 27, bayan Mbappe, in ji (Independent) .
Barcelona tana shirin karbar tayin fan miliyan 81 daga Paris St-Germain kan dan wasan tsakiyarta, Ivan Rakitic, mai shekara 30, in ji jaridar (Sport ta Express) .
Real Madrid tana neman tsohon dan wasan gaban Liverpool Iago Aspas, mai shekara 31, a wata yarjejeniyar fan miliyan 35, in ji (Super Deporte ta HITC) .
Real Betis ta nemi dan wasan
Manchester City mai shekara 21 ,
Oleksandr Zinchenko, ya buga mata wasan aro na kaka daya da nufin komawa kulob din a kan yarjejeniyar din-din-din, in ji (Mundo Deportivo ta Manchester Evening News) .
Koci Marco Silva ya ce dan wasna gefen
Everton, Ademola Lookman, shi ne "dan wasan da kulob din ke ji da shi a yanzu da kuma gaba" domin hana RB Leipzig ci gaba da zawarcin dan wasan dan Ingila, mai shekara 20, kamar yadda jaridar
(Independent) ta ruwaito.