Jama'a su yi koyi da jami'an tsaron Legas – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yaba wa wasu jami'an tsaro biyu na filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas dangane da kawo wata jaka makare da kudade da sauran abubuwa masu muhimmanci da wata fasinja ta manta.
Shugaban ya ce wadannan jami'an tsaro wato Francis Emepueaku da Achi Daniel, sun yi "namijin kokari," san nan kuma sun nuna halayya ta gari wadda za ta zamo "abin kwatance, kuma abin da ya kamata sauran jama'a su yi koyi ne."
Gaskiya da amannar da jami'an tsaron suka nuna, ta sanya shugaban fitar da sanarwa inda ya ce sun zamo abin koyi ga dukkan 'yan Najeriya.
Muhammadu Buhari ya ce "Gaskiya da rikon amana ita ce hanya madaidaiciya ga dukkan 'yan Najeriya, kuma yana da kyau a duk inda muke ko kuma kowanne irin mukami muke rike da shi mu rinka kwatanta gaskiya."
Jakar dai ta wani likita ce mazaunin jihar Lagos wato Dokta Banji Oyegbami wanda ya dawo daga Amurka, wadda aka manta a filin jirgin saman, kuma tana dauke da abubuwa da suka kunshi makudan dalolin Amurka da wayar salula da agogon hannu mai tsada da kuma sauransu.
Har ila yau jami'an tsaron dai sun ki karbar kudin tukwicin da aka ba su, inda suka ce "sun yi aikin da ya rataya ne a kansu."
Yaki da cin hanci da rashawa, na daga cikin manyan manufofin da shugaban ya ce ya fi bai wa fifiko a cikin mulkinsa.