Online counter

Fara wa da iyawa: PDP ta nada Saraki a matsayin sabon jagoranta

Fara wa da iyawa: PDP ta nada Saraki a matsayin sabon jagoranta

A yau, Alhamis, ne jam’iyyar PDP ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki na farko tun bayan dawowar wasu ‘ya’yanta daga jam’iyyar APC.
Jam’iyyar ta PDP ta nada Bukola Saraki a matsayin sabon jagoranta na kasa, mukamin da mataimakinsa, Ike Ekweremadu, ke rike das hi kafin ya canja sheka cikin ranar Talata.
Taron ya samu halartar Saraki, Rabi’u Kwankwaso, gwamna Aminu Tambuwal da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe.
Fara wa da iyawa: PDP ta nada Saraki a matsayin sabon jagoranta
Saraki da Tambuwal a wurin taron PDP
Shigowar Saraki ta jawo kaurewar sowa da ihun murna daga shugabannin PDP. Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ne ya jagoranci Saraki shiga wurin taron.
An hangi Saraki da Tambuwal sun rungume juna yayin da suka hadu a wurin taron na PDP. Saraki da Tambuwal sun fita daga APC ne cikin wannan satin da muke ciki.
Bayan shugabannin PDP da sabbin ‘ya’yanta da suka tsallako daga APC, taron ya samu halartar gwamnoni, ‘yan majalisu da kuma wasu daga cikin masu burin yiwa jam’iyyar takarar shugaban kasa.

Post a Comment

0 Comments