Da gaske Atiku ya fi Buhari iya motsa jiki?

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari shagube kan ikirarin da ya yi cewa motsa jikin da ya yi ya ba shi damar kimtsawa domin fuskantar zaben 2019.
Ranar Talata ne dai shugaban kasar ya halarci filin sallar Idi a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, sannan ya yi tafiyar mita 800 a kasa daga masallacin zuwa gidansa bayan an sauko daga Idi.
Daga bisani ne mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya fitar da sanarwar da ke cewa "takawar da Shugaba Buhari ya yi a kasa daga masallaci zuwa, cike da sowa da tafin magoya baya, ya nuna cewa duk wanda yake shakkun koshin lafiyar shugaban ya kamata ya sake nazari."
Wasu na gani fadar shugaban kasar ta yi wannan kalami ne domin yin raddi ga masu cewa Shugaba Buhari ba shi da koshin lafiyar sake tsayawa takara a zaben 2019.
Me ya faru a Nigeria tun da Shugaba Buhari ya tafi hutu?
Shin Osinbajo ya kama hanyar maye gurbin Buhari?
'Ina motsa jiki a ko da yaushe'
Sai dai a wani sakon Twitter da Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa anda ake ganin tamkar shagube ga kalaman fadar shugaban Najeriya, ya ce motsa jiki ba shi ne ma'unin iya mulki ba.
"A ko da yaushe ina yin sassarfa da motsa jiki na tsawon mil daya amma ina ganin bai dace hakan ya zama ma'aunin da zan yi amfani da shi wurin neman kuri'ar 'yan Najeriya ba. Ina son jam'iyyata, PDP da kuma 'yan Najeriya su zabe ni saboda na yi aiki ba motsa jiki ba. Ba zan yi tafitar da za ta zama maras amfani ba."
Sau biyu dai Shugaba Muhammadu Buhari yana tafiya jinya London tun da ya zama shugaban kasa a 2015.
Hakan ya sa 'yan kasar da dama na ganin shugaban, mai shekara 75, ba shi da cikakkiyar koshin lafiyar sake yin mulki a wa'adi na biyu.
Sai dai fadarsa da ma mukarrabansa sun sha cewa Shugaba Buhari ya murmure sosai kuma a shirye yake ya sake jagorantar kasar.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London
Ga wasu karin labarai da za ku so karanatawa: