Online counter

Buhari ya fake da tafiya hutu ne bayan gama kitsa yadda za a tsige Bukola – PDP

Buhari ya fake da tafiya hutu ne bayan gama kitsa yadda za a tsige Bukola – PDP

A gobe Juma’a, 3 ga watan Agusta, shugaba Buhari zai tafi kasar Ingila inda zai shafe tsawon kwanaki 10 a hutunsa da zai yi na shekara.
Sai dai batun tafiyar hutun na shugaba Buhari ya saka jam’iyyar adawa PDP cikin tararrabi tare da zargin cewar Buhari zai fice daga Najeriya ne bayan ya kamala kitsa yadda za a cire shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, saboda ya fita daga jam’iyyar APC.
A wani jawabin PDP ta fitar tab akin ta bakin sakataren tan a yada labarai, Kola Ologbondiyan, jam’iyyar ta ce tana sane sarai da makircin da shugaba Buhari ya gama kullawa tsakaninsa da gwamnoni da kuma Sanatocin APC domin tsige Bukola Saraki.
Buhari ya fake da tafiya hutu ne bayan gama kitsa yadda za a tsige Bukola – PDP
Buhari da Bukola
A daren ranar Laraba ne shugaba Buhari ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC, karkashin jagorancin gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Kafin ganawarsa da gwamnonin, shugaba Buhari ya gana da sanatocin APC da shugabancin jam'iyyar a fadar ta sa.
Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewar shugaba Buhari da ragowar shugabannin jam’iyyar sun amince cewar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya kamata a ajiye mukaminsa, tun da ya bar jam’iyyar.

Post a Comment

0 Comments