Buhari ba ya jin shawara – Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ringa yin biris da shi a duk lokacin da ya je masa da wata shawara ta gyara.
Atiku Abubakar ya shaida wa Jimeh Saleh na BBC Hausa cewa idan ya zama shugaban kasa zai samarwa matasa aiki fiye da gwamnatin Buhari.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu an kasa samunsa da laifin cin hanci da rashawa da wadansu ke zarginsa da aikatawa.