Bene ya rufta da mutane a Abuja

Jami'an ba da agajin gaggawa a Najeriya na yunkurin ceto wasu mutane da wani bene mai hawa biyar ya rufta da su a Abuja ranar Juma'a.
Kimanin mutane hudu ne aka ba da rahoton cewa an garzaya da su asibiti.
Ginin ya rufta ne da yammacin Juma'ar a unguwar Jabi.
Wakilin BBC Abdulwasiu Hassan wanda ya je wajen ya ce, ginin yana da girma, kuma ana aiki a cikinsa ne lokacin da ya rufta.
Ya ce duk da ruwan sama da ake tafkawa, jami'an agaji sun dukufa wajen ceto mutane da suka makale.
"A yanzu haka ana kokarin janye karfen da ake amfani da su wajen gini, domin samun damar kwashe baraguzan ginin da ya danne mutane", in ji Abdulwasiu.
Da gaske ne EFCC ta samu kudi a gidan Lawal Daura?
Birtaniya ta tura sojojinta aikin hajji
An kirkiro nama a dakin binciken kimiyya
Wasu bayanai na cewa cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da mata.
Kawo yanzu ba a san adadin mutanen da ke cikin baraguzan ginin da ya rufta ba.
San nan kuma hukumomi ba su kai ga karin bayani kan musabbabin faduwar ginin ba.
Sai dai alamu na nuna cewa ginin ya rufta ne baki dayansa.
Tuni dai jami'an agaji suka dukufa domin ceto mutane da lamarin ya shafa.
Sai dai mai yuwawa a fuskanci tsaiko wajen aikin ceton, sakamakon ruwan sama da ake yi a birnin a lokacin da ake yunkurin ceto mutane.