Ba don na burge mutane na yi tafiyar kafa ba a Daura
– Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya ce ba don ya burge kowa ya yi tattaki daga masallacin idi zuwa gidansa ba a Daura ranar Sallah.
Shugaba ya yi tafiyar kusan kilomita daya a kafa bayan idar da sallar Idi ranar Talata.
Wasu makusantan shugaban sun yi alfahari da tattakin da ya yi na mita 800, inda suka ce hakan na nuna yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya ci gaba da shugabancin Najeriya har zuwa 2023.
Sai dai batun ya janyo ce-ce ku-ce tsakanin 'yan siyasa, inda masu hamayya da shi ke ganin babu wani abin burge wa a cikin tattakin na Buhari.
A wani mataki mai kama da shagube, tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, ya ce shi yana tafiyar sama a kilomita daya, kuma bai ga abin birge wa ga dan siyasa ya ringa bayyana cewa ya yi tafiyar kafa ba.
Buhari ba ya jin shawara – Atiku Abubakar
Buhari ya ce hakura da yaki da rashawa cin amanar 'yan Najeriya ne
Ya ce 'yan Najeriya aiki suke bukata ba tafiyar kafa ba, kuma idan ya samu damar shugabanci aiki zai yi, ba wai yayata cewa ya yi tafiyar kafa ba.
To sai da a sakon Twitter da shugaba Buharin ya wallafa ranar Juma'a ya bayyana cewa, bai yi tattakin don ya nuna wa mutane cewa yana da cikakakkiya lafiya ba.
Ya ce ya yi tattakin ne saboda ya gana da mutanen mazabarsa.
"An yi ta surutai a kan tattakin da na yi a Daura 'yan kwanakin da suka gabata. Ban yi tafiyar kafan ba don nuna wa wani cewa ina da cikakkiyar lafiiya," in ji Buhari.
Ya kara da cewa, "Daruruwan mutane mazabata sun fito domin su yi ido hudu da ni, sannan an lullube tagar motar da na ke ciki da bakar leda. Don haka ne na yanke shawarar fito wa daga motar don mutane su gan ni."
"Mutanen da suka san ni sun san cewa ba na yin wani abu don na kara farin jinin siyasa," a cewar Buhari.
Shugaba Buhari ya kara da cewa ba sai ya yi tattaki domin ya gamsar da mutane cewa yana da lafiya ba, kuma bai yi haka a matsayin hujja ta sake neman tsayawa takara ba.