Ana dakon sakamakon zabukan da hukumar zaben Najeriya ta gudanar a wasu mazabu da ke cikin jihohi hudu na kasar.

Da safiyar yau aka fara gudanar da zabukan kamar haka:
1. Zaben sanata a gundumar arewacin jihar Katsina
2. Zaben sanata a gundumar kudancin jihar Bauchi
3. Zaben dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja-Kogi na jihar Kogi
4. Zaben dan majalisar jiha na mazabar Obudu a jihar Kuros Riba
Zaben 2019 sai ya fi na 2015 nagarta — INEC
Yaushe majalisar dokokin Najeriya za ta koma zama?
A jihar Katsina, wani yaya da kaninsa ne ke takarar kujerar sanata ta arewacin Katsina wato yankin Daura a dalilin rasuwar tsohon sanata Mustapha Bukar.
A jihar Bauchi kuwa, 'yan takara tara ne ke neman darewa kujerar sanatan gundumar kudancin jihar.
Sun hada da Lawal Yahaya Gumau (APC), sai Isah Yuguda (GPN), sai Haruna Ayuba (ADC), da Aminu Tukur (APP) da kuma Usman Hassan (Kowa Party).
Sauran sun hada da Maryam Bargel (SDP) da Husseini Umar (NNPP) da Usman Chaledi (PDC) da kuma Ladan Salihu (PDP).
Kamar jihar Katsina, duk wanda yayi nasara zai maye gurbin tsohon sanatan yankin ne, Sanata Ali Wakili wanda ya rasu a watan Maris na bana.
A jihar Kogi an gudanar da zabe ne domin maye gurbin tsohon sanatan yankin wanda wata babbar kotu ta sauke daga mukaminsa.
Sanata Atai Aidoko ya rasa mukaminsa ne saboda kotu ta gano cewa ya tafka kura'kurai wajen samun tikitin tsayawa takara a karkashin jam'iyyarsa ta PDP.
A jihar Kuros Riba da ke kudu maso gabashin Najeriya kuwa, an gudanar da zaben dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Obudu ne.
Mazabar ba ta da wakili tun bayan mutuwar wakilinsu Mista Stephen Ukpukpen a karshen watan Mayun bana.
Tuni dai aka gudanar da zabubbukan kuma a halin yanzu ana dakon sakamako ne a wadannan mazabu hudu da ke cikin jihohi uku na arewacin Najeriya da daya da ke udu maso gabashin kasar.
Hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa wadanda suka kada kuri'unsu sun zarce mutum miliyan biyu a cikin kanana hukumomi 22 na jihohi hudun.