'An shawo kan sojojin da suka yi bore a Maiduguri'

Rundunar da ke yaki da Boko Haram da aka yi wa lakabi Operation lafiya dole ta ce kura ta lafa bayan bore da wasu sojoji suka yi a filin jirgin saman Maiduguri, ranar Lahadi.
Ta ce shugaban rundunar Janaral Abba Dikko ya shiga tsakani kuma ya yi wa sojojin bayani.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar, Kanal Onyema Nwachukwu ta ce za a dauki mataki, domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
Bayyanai sun ce sojojin da ke fada da kungiyar Boko Haram sun shafe kusan sa'o'i hudu suna harbi sama tare da yin barazana ga kwamandojinsu.
Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu daga cikin sojojin na cewa fushi ne shi ya sa suke harbi, suna cewa basu ga dalilin da zai sa a dauke su zuwa wani wuri ba bayan sun yi shekaru hudu a Maiduguri.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce wasu tsiraru ne suka yi boren saboda matakin da aka dauka na turasu fagen daga.
Ta ce an dauki matakin ne bayan nazarin da rundunar ta yi kan yanayiin tsaro a yankin .
"An dauki matakin ne bayan nazari na baya-baya nan da aka yi kan yanayin tsaro a yankin. Sai dai abin takaici wasu sojoji tsiraru basu fahimci dalilin da yasa aka dauki wannan matakin ba , sun dauka zai shafi yawan shekaru da za su yi suna aiki , shi yasa suka fusata suka rika harbi sama". in ji sanarwar.
"Kwamadan rundunar ya kuma bayar da umarni ayi bincike akan dalilan da yasa sojojin suka yi harbi a sama maimakon su bi matakan da suka dace don mika kokensu".
Sojojin Najeriya sun yi bore a Maiduguri
Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya biyar
Sai dai akwai rahotanin da ke cewa ana ci gaba da samun karuwa a yawan sojojin da suke da damuwa a kan yadda ake tafiyar da shirin yaki da Boko Haram, duk da cewa gwamnatin kasar ta yi ikirarin karya lagwon mayakan kungiyar tun daga shekarar 2015.
Amma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.