An rufe filin jirgin saman Seattle bayan da wani ya sace jirgin sama

Wani ma'aikacin kamfanin jirgin sama ya sace wani jirgin fasinja daga filin jirgin sama na birnin Seattle a Amurka, kuma jirgin ya fadi a wani tsibiri dake kusa.
Jami'ai a filin jirgin saman sun ce mutumin da ya sace jirgin a jiya Jumma'a, ya tashi da shi ne ba tare da izini ba.
A sanadiyyar aukuwar wannan lamarin an rufe filin jirgin sama na Seattle-Tacoma International.
Wasu jiragen yaki biyu samfurin F-15 sun bi jirgin wanda daga baya ya fado a Puget Sound. Jami'ai sun ce da alama matukin jirgin ya mutu nan take.
Kun san yadda za ku tsira daga hadarin jirgin sama?
Wata mata ta bar jaririn da ta haifa a jirgin sama
Mutum 66 sun mutu a hatsarin jirgin sama na Iran
Ofishin 'yan sandan garin ya ce lamarin "ba aikin ta'addanci ba ne", kuma sun ce mutumin mai shekara 29 da haihuwa sananne ne a garesu.
Jirgin samfurin Bombardier Q400 mai injuna biyu mallakin kamfanin Horizon Air ne.
An tura wasu jiragen yaki biyu nan take, kuma bidiyon da wasu 'yan kallo suka nada na nuna jiragen yakin na bin jirgin da aka sace.
Shin me yasa ya saci jirgin?
Ana ganin mutumin da ya saci jirgin yayi haka ne saboda ya burge kawai.
Sautin da jami'ai suka nada a lokacin da suke magana da mutumin ya tabbatar da haka.
An kuma ji mutumin na nuna damuwarsa saboda rashin isasshen mai a cikin jirgin.
Ya kuma ce zai iya sauka da jirgin da kansa saboda ya iya "tuka jiragen sama na cikin wasannin komfuta".
A cikin sautin an kuma ji mutumin na cewa:
Ya na sha'awar zuwa dutsen Olympic Mountain da ke jihar Washington domin ya sha kallo
Ko zai iya yin wasa da jujjuya jigin kamar mazari kafin ya sauka
Yana fatan kamfanin da suka mallaki jirgin za su dauke shi aiki a matsayin direban jirgi idan har ya koma da jirgin ba tare da wata matsala ba