Online counter

2019: Gwamnonin PDP 3 daga kudu zasu koma APC

2019: Gwamnonin PDP 3 daga kudu zasu koma APC

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin arewata tsakiya, Alhaji Suleiman Ahmed Wambai, ya bayyana cewar a cikin kwana uku masu zuwa wasu gwamnonin PDP daga yankin kudu maso gabashin Najeriya zasu tsallaka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Wambai ya yi furuci ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da aka yi a gidan gwamnatin jihar Nasarawa dake Lafiya, babban birnin jihar.
An yi taron ne domin nunawa tare da jaddada goyon bayan takarar shugaba Buhari a zaben shekarar 2019 mai zuwa.
A jawabinsa, gwamna Tanko Almakura, na jihar Nasarawa ya bukaci magoya bayan APC das u kara jazircewa tare da basu tabbacin cewar nasara tana tare da jam’iyyar a zabukan shekarar 2019 da za a yi.
2019: Gwamnonin PDP 3 daga kudu zasu koma APC
Taron shugabannin APC
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sanata Abdullahi Adamu kuma tsohon gwamnan jihar da masu son yin takarar gwamna a jam’iyyar da kuma dukkan mambobn majalisar dokokin jihar.
A wani labarin mai alaka da wannan, kun ji cewar Abdulmumin Jibrin Kofa, dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomi Kiru da Bebeji a jihar Kano, ya yi ikirarin cewar akwai gwamnonin jam'iyyar PDP 4 dake aiki tare da jam'iyyar APC domin ta kai ga nasara a zaben 2019
Duk da bai ambaci sunayen gwamnonin ba, Kofa ya bayyana cewar akwai yarjejeniya tsakaninsu da jam'iyyar APC a kan goyon bayan takarar shugaba Buhari a zaben shekarar 2019.
Da yake ganawa da manema labarai a Abuja a jiya, Laraba, Kofa ya ce, "a halin yanzu akwai gwamnonin jam'iyyar PDP 4 zuwa 5 da aka kulla yarjejeniyar goyon bayan takarar shugaba Buhari da su a zaben shugaban kasa."

Post a Comment

0 Comments