Online counter

Yanzu Yanzu: PDP ta hade da jam’iyyu sama da 30 ta chanja suna zuwa jam’iyyar CUPP

Yanzu Yanzu: PDP ta hade da jam’iyyu sama da 30 ta chanja suna zuwa jam’iyyar CUPP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli ta hade da jam’iyyun siyasa sama da guda 30 ta sanar da sabon sunanta a matsayin jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP).
A cewar gidan talbijin din Channels, sanarwan na zuwa ne bayan kulla yarjejeniyar fahimta da shugabannin jam’iyyun da suka hade suka yi.
Hakan duk kokari ne na son ganin sun kayar da jam’iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a zaben 2019 mai zuwa.
Wadanda suka halarci taron wanda aka gudanar a cibiyar Musa Yar’adua dake Abuja sun hada da jam’iyyar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo African Democratic Congress (ADC), Social Democratic Party of Nigeria (SDP), National Conscience Party (NCP), Labour Party, da sauran sabbin jam’iyyun da aka yiwa rijista.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Uche Secondus, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, shugaban kungiyar R-APC, da kuma Sanata Dino Melaye.

Post a Comment

0 Comments