Online counter

Yan majalisa na bukatar a canja jadawalin zaben hukumar INEC saboda aikin hajji

Yan majalisa na bukatar a canja jadawalin zaben hukumar INEC saboda aikin hajji

Majalisar wakilai na tarayya ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC tayi gyara jikin jadawalin zaben 2019 saboda ta bawa 'yan majalisar damar zuwa Saudiyya don sauke farali.
Wannan rokon ya biyo bayan wata kudiri ne da Honarabul Abdullahi Balarabe Salame daga jihar Sakkwato ya gabatar a gabar majalisar.
A yayin da yake gabatar da kudirin, Hon. Salame yace a jadawalin na INEC, za'a gudanar da zaben fidda gwanaye kwanaki biyu kafin Arafat da za'a fara a ranar Litinin 20 ga watan Augustan 2018 kuma a kammala a ranar 21 ga watan Augustan 2018.
'Yan majalisa na bukatar a canja jadawalin zaben hukumar INEC saboda aikin hajji
'Yan majalisa na bukatar a canja jadawalin zaben hukumar INEC saboda aikin hajji
Ya ce majalisar ta fahimci cewa a jadawalin zaben da INEC ta fitar, za'a fara gudanar da zabben fida gwanaye na shugaban kasa da 'Yan majalisun tarayya a ranar 18 ga watan Augustan shekarar 2018.
Salame yace hallartar Arafat yana daya daga cikin shika-shikan aikin Hajji saboda hakan rashin hallartar tsayuwar Arafat zai kawo nakasu ga aikin Hajji maniyata.
Majalisar ta saurari kudirin kuma ta amince dashi bayan yan majalisar sun kada kuri'arsu.
A wata rahoton, 24blog.com.ng ta kawo muku yadda wani hakimi mai suna Ibrahim Madawaki ya sadaukar da ransa saboda ya kare rayyukan mutanensa.
Matawalle ya fusakanci yan bindigan ne kuma ya ki amincewa ya hau babur ya bisu zuwa daji wadda hakan yasa suka fara dukkansa amma ya nemi alfarmar cewa idan har zasu kashe shi, su aikata hakan ba tare da yiwa al'ummarsa komai ba.

Post a Comment

0 Comments