Online counter

Yan Boko Haram sun ga ta kansu: Sojin saman kasar nan ta yi musu barin wuta (Bidiyo)

Yan Boko Haram sun ga ta kansu: Sojin saman kasar nan ta yi musu barin wuta (Bidiyo)

- Cikin salo na kwarewa da sanin makama Sojojin saman Najeriya sun yiwa 'yan Boko Haram lugudan wuta ta sama
- Jirgin saman ya gama kalle su cikin tsanaki kafin daga bisani ya zuba musu ruwan wutar da yayi sanadin kashe su da yawan gaske
Rundunar sojin saman kasar nan a yau Litinin sun bayyana nasarar da suka samu wajen kashe mayakan Boko Haram da yawa a wani hari da suka kai ta hanyar yi musu ruwan wuta daga sama, a kudu maso yammacin karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar sojin Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ne ya bayyana haka, a wani jawabi da ya fitar. Ya ce rundunar tasu tayi bincike tare da gano ‘yan tada kayar bayan da yawa a yankin.
Ya kara da cewa, cikin tsanaki aka kai farmakin ba tare da sun sani ba, domin dakile cigaba da kawo wa Sojoji hari.
"Rundunar Air task force, wato wani yanki na sojin sama wanda suke hadin guiwar shirin ‘Lafiya Dole’, sun kai harin a kauyen Tongule dake kudu maso yammacin karamar hukumar Dikwa, wanda aka samu gagarumar nasara".
"Yayin harin da aka kai ta hanyar jiragen sama an kashe da dama daga mayakan na Boko Haram, sai kuma kadan daga ciki da suka yi yunkurin guduwa wanda suma aka yi nasarar kashe su". Daraktan yada labaran rundunar ya shaida.

Post a Comment

0 Comments