Online counter

Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta

Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta

- Sojojin Najeriya sun samu nasarar kawato bindigu da harsasai a hannun 'yan Boko Haram
- Bayan makaman kuma sunyi nasarar kwato wata yarinya da suka gudu suka barta
- Kamar yadda kakakin rundunar ya tabbatar
Rundunar sojin kasar nan a jihar Borno sun yi nasarar kubutar da wata yarinya daga hannun yan tada kayar baya na Boko Haram, kamar yadda mai magana da yawun bakin Rundunar sojin Birigediya-Janar Texas Chukwu ne ya bayyana hakan a yau litinin.
Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta
Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta
Chukwu ya yi wannan jawabin ne a wani sumaman sharar daji da suka yi "An samu bindigogi kirar AK47 har guda uku sai kuma tarin harsashi mai yawa tare da riga mai dauke da bam".
"An samu kayan hada bam da dama wanda suka hada da batirin waya, da bam din hannu, sai batirin mota kirar volt guda biyu da sauran abubuwan kayan hada bam". Kamar yadda kamfanin dillacin labarai (NAN) ya rawaito.

Post a Comment

0 Comments