Online counter

Wani dattijo mai shekaru 60 ya maka wata budurwa a kotu saboda taki aurensa

Wani dattijo mai shekaru 60 ya maka wata budurwa a kotu saboda taki aurensa

Wani tsoho mai shekaru 60, Salisu Nuhu, ya yi karar budurwarsa, Janet Baru a kotu saboda ta ki amincewa da aure shi.
Mai shigar da karar ya shaidawa kotun Shari'a na II na magajin gari cewa budurwarsa Janet tayi masa alkawarin tana kaunarsa kuma zata musulunta ta aure shi amma daga baya da canja magana bayan karbe masa kudade da yawa.
Ya kara da cewa budurwar tasa ta hada baki da kawarta mai suna Janet inda suka karbe N30,000 a hannunsa bayan tayi masa alkawarin zata aure shi.
Wani dattijo mai shekaru 60 ya maka wata budurwa a kotu saboda taki aurensa
Wani dattijo mai shekaru 60 ya maka wata budurwa a kotu saboda taki aurensa

"Mun kawashe shekaru hudu muna soyaya da Janet kuma duk lokacin da na ziyarce ta, na kan bata N1,000 ko N2,000 kuma ko hannunta ban taba rikewa ba.
"Kawarta ta Juliet tace min in baiwa Janet N40,000 saboda in nuna mata da gaske nake zan aureta amma N30,000 na bata," inji shi.
Ya kara da cewa ta nemi ya tafi kauyensu a Benue don ya gana da iyayenta amma bai samu ikon zuwa ba sai dai ya biya wa dan uwanta kudin mota N5,000 don ya iso Kaduna su gana.
Mr Nuhu ya bayyana cewa lokacin bikin Kirsimeti ya bawa Janet N45,000 tare da atamfa na N8,000 da kuma kudin dinki N2,000.
Ya roki kotu ta taimaka ta karbo masa kudaden da ya kashe a kanta.
A bangarenta, Janet ta ce shekara daya kawai su kayi suna soyaya kuma ta ce N75,000 ta taba karba daga hannunsa a duk tsawon lokacin da suka kwashe suna soyaya.
Janet ta shaidawa kotu cewa bata mayar masa da kudin ba saboda ya bada ne a matsayin kyauta ba sadaki ba.
Bayan sauraran mai karar da wanda akai kararta, Alkalin Kotun, Musa Sa'ad, ya dage shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Yuli don yanke hukunci.

Post a Comment

0 Comments